25 Nuwamba 2020 - 18:05
Mutane 17 Sun Mutu Sakamakon Wasu Tagwayen Hare-Hare A Garin Bamiyan Na Afghanistan

Alal akalla mutane 17 ne suka mutu kana wasu da dama kuma suka sami raunuka sakamakon wasu tagwayen hare-hare da aka kai garin Bamiyan na kasar Afghanistan da mafiya al’ummar wajen ‘yan Shi’a ne.

ABNA24 : Yayin da yake magana kan hakan, kakakin Ma’aikatar cikin gidan Afghanistan din Tariq Arian ya ce lamarin ya faru ne a wajen wata kasuwa a daidai lokacin da jama’a suke ci gaba da hada-hadarsu a yammacin jiya Talata lokacin da abubuwan fashewar da aka dana suka fashe a wajaje biyu.

Kafar watsa labaran Tolo News ta kasar Afghanistan din ta jiyo wata majiyar ‘yan sanda tana cewa an boye abubuwan fashewar da suka tashi din ne a wani waje a gefen kasuwar inda bayan fashewar mutane da dama suka rasa rayukansu mafiyawan su fararen hula. Wasu rahotannin sun ce daga cikin mutane 17 da aka tabbatar da mutuwarsu, 15 daga cikinsu fararen hula ne sai kuma wasu ‘yan sandan ba da hannu guda biyu.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin ta’addancin.

A shekarun baya dai ‘yan Shi’an wannan yankin sun fuskanci irin wadannan hare-hare da ‘yan ta’adda suke kai musu a garuruwan da suke ciki kuwa har da birnin Kabul.

Kasar Afghanistan din dai tana ci gaba da fuskantar irin wadannan tashin hankali duk kuwa da ci gaba da tattaunawar sulhu da ke gudana tsakanin gwamnati da kungiyar Taliban a kasar Qatar.

342/